Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 2:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Abigail ta haifi Amasa. Mahaifin Amasa shi ne Yeter daga zuriyar Isma'ilu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Abigiyel ita ce mahaifiyar Amasa, wanda mahaifinsa shi ne Yeter mutumin Ishmayel.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 2:17
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Absalom ya naɗa Amasa ya zama shugaban sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan Yeter ne, Ba'isma'ile, wanda ya auri Abigail 'yar Nahash, 'yar'uwar Zeruya mahaifiyar Yowab.


Ubangiji zai ɗora masa alhakin mugayen ayyukansa, gama ya kashe mutum biyu ba da sanin tsohona Dawuda ba, waɗanda kuma suka fi shi adalci, wato Abner ɗan Ner, shugaban sojojin Isra'ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban sojojin Yahuza.


“Ka kuma san abin da Yowab ɗan Zeruya ya yi mini, yadda ya kashe shugabannin sojoji na Isra'ila su biyu, wato Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya zubar da jinin yaƙi a lokacin salama. Ya sa jinin yaƙi a kan ɗamararsa wadda take gindinsa, da kuma kan takalmansa da yake ƙafafunsa.


Ku ce wa Amasa, ‘Ashe, kai ba ƙashina da namana ba ne? Allah ya hukunta ni idan ba kai ne shugaban rundunar sojojina a maimakon Yowab ba.’ ”


'Yan'uwansu mata kuwa su ne Zeruya da Abigail. 'Ya'yan Zeruya, maza, su ne Abishai, da Yowab, da Asahel, su uku ke nan.


Azuba, matar Kalibu ɗan Hesruna ta haifa masa 'ya'ya maza. Matarsa Yeriyot kuma ta haifi 'ya'ya maza, su ne Yesher, da Shobab, da Ardon.


Ruhun Allah kuwa ya sauko a kan Amasa wanda daga baya ya zama shugaban talatin ɗin, sai ya ce, “Muna tare da kai, ya Dawuda ɗan Yesse! Allah ya ba ka nasara tare da waɗanda suke tare da kai! Allah yana wajenka!” Sa'an nan Dawuda ya marabce su, ya maishe su shugabanni a sojojinsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ