Sai Dawuda ya ce, “Duk wanda ya ci Yebusiyawa da fari shi ne zai zama babban shugaban sojoji.” Yowab ɗan Zeruya ne ya fara tafiya, domin wannan aka maishe shi shugaba.
Suka yi ijarar karusai dubu talatin da dubu biyu (32,000), da Sarkin Ma'aka, tare da jama'arsa. Suka zo suka kafa sansani a gaban Medeba. Ammonawa kuwa suka tattaru daga biranensu don su yi yaƙi.