Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 19:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Waɗansu mutane kuwa suka je suka faɗa wa Dawuda abin da ya sami mutanen. Sai ya aiko a tarye su, gama an ƙasƙanta mutanen nan da gaske. Sai sarki ya ce, “Ku zauna a Yariko, har lokacin da gyammanku suka tohu sa'an nan ku iso.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Da wani ya zo ya faɗa wa Dawuda game da mutanen, sai ya aiki ’yan aika su sadu da su, gama an ƙasƙantar da su ainun. Sarki ya ce, “Ku zauna a Yeriko har sai gemunku sun yi girma, sa’an nan ku dawo.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 19:5
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da abokan bautarsa suka ga abin da ya faru, suka yi baƙin ciki gaya, har suka je suka gaya wa ubangidansu duk abin da ya gudana.


A cikin kwanakinsa, Hiyel mutumin Betel ya gina Yariko. Ya yi hasarar ɗan farinsa, Abiram, sa'ad da ya kafa harsashin ginin, ya kuma yi hasarar autansa, Segub, sa'ad da ya sa ƙofofin, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Joshuwa ɗan Nun.


Hanun kuwa ya kama fādawan Dawuda, ya aske gyammansu, ya yanyanke rigunansu a tsaka daga wajen kwankwaso, sa'an nan ya sallame su.


Sa'ad da Ammonawa suka ga sun mai da kansu abin ƙi ga Dawuda, sai Hanun da Ammonawa suka aika da talanti dubu (1,000) na azurfa don su yi ijara da karusai da mahayan dawakai daga Mesofotamiya, da jihohin Ma'aka ta Suriya, da Zoba.


Da aka faɗa wa Dawuda sai ya aika a tarye su, gama mutanen sun sha kunya ƙwarai. Sarki Dawuda ya ce musu su zauna a Yariko har gyammansu su toho, sa'an nan su komo.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ