1 Tarihi 18:8 - Littafi Mai Tsarki8 Dawuda kuma ya kwaso tagulla mai yawan gaske daga Beta da Berotayi, biranen Hadadezer. Da su ne Sulemanu ya yi kwatarniya, da ginshiƙai, da kayayyakin Haikali. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Daga Teba da Kun, garuruwan da suke ƙarƙashin Hadadezer, Dawuda ya kwashe tagulla da yawa sosai, wanda Solomon ya yi amfani don yă yi Tekun tagulla, ginshiƙai da kuma kayayyakin tagulla dabam-dabam. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Da wahala mai yawa na yi tanadi domin Haikalin Ubangiji, zinariya wajen talanti dubu ɗari (100,000), da azurfa kuma wajen talanti zambar dubu (1,000,000), domin gina Haikalin Ubangiji. Bayan wannan akwai tagulla da ƙarfe masu tarin yawa. Na kuma tanada katakai da duwatsu. Kai kuma sai ka ƙara a kansu.
Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da daruna. Huram kuwa ya gama dukan aikin da ya alkawarta wa sarki Sulemanu a Haikalin Allah: ginshiƙi biyu dajiya biyu a kan ginshiƙi biyu siffar tukakkiyar sarƙa a kan kowane ginshiƙi Siffar rumman guda ɗari huɗu domin raga don rufe dajiyar ginshiƙan dakali goma daro goma kwatarniya. Bijimi goma sha biyu da suke ɗauke da kwatarniya kwanoni, manyan cokula masu yatsotsi, wato ya yi dukan kayan nan da tagulla domin Haikalin Ubangiji.