Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 18:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Dawuda kuma ya ci Hadadezer, Sarkin Zoba, da yaƙi a Hamat, sa'ad da ya tafi ya kafa mulkinsa a Kogin Yufiretis.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Ban da haka, Dawuda ya yaƙi Hadadezer sarkin Zoba, har can Hamat, sa’ad da ya je don yă kafa mulkinsa a wajen Kogin Yuferites.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 18:3
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka rabu da mu, ya Allah, har aka ci nasara a kanmu, Ka yi fushi da mu, amma yanzu sai ka juyo wurinmu!


Dawuda kuma ya ci Hadadezer ɗan Rehob, Sarkin Zoba, da yaƙi lokacin da shi Hadadezer yake kan tafiya zuwa Kogin Yufiretis don ya tabbatar da ikonsa a wurin.


Da Ammonawa suka ga sun sa Dawuda ya yi gāba da su, suka yi sufurin Suriyawan Bet-rehob da na Zoba, mutum dubu ashirin (20,000), suka kuma yi sufurin Sarkin Ma'aka da mutanensa dubu ɗaya, da mutanen Ish-tobi dubu goma sha biyu (12,000).


Sa'ad da Saul ya ci sarautar Isra'ila, ya yi yaƙi da dukan abokan gābansa da suke kewaye da shi. Ya yi yaƙi da Mowabawa da Ammonawa, da Edomawa, da sarakunan Zoba, da Filistiyawa. Duk inda ya yi yaƙi ya sami nasara.


Zan yanka muku kan iyaka daga Bahar Maliya zuwa tekun Filistiyawa, daga jeji kuma zuwa Kogin Yufiretis. Gama zan ba da mazaunan ƙasar a hannunku, za ku kore su daga gabanku.


A wannan rana Ubangiji ya yi wa Abram alkawari ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga Kogin Masar zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis ke nan,


Ya kuma ci Mowab da yaƙi, Mowabawa suka zama bayin Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji.


Sai Dawuda ya ƙwace karusai dubu (1,000), da mahayan dawakai dubu bakwai (7,000), da sojojin ƙasa dubu ashirin (20,000) daga gare shi. Dawuda kuma ya yanyanke agarar dawakan da suke jan karusai, amma ya bar waɗansu dawakai daga cikinsu waɗanda suka isa jan karusai ɗari.


Manya manyan sarakuna sun yi sarauta a Urushalima, waɗanda suka yi mulki a kan dukan lardin Yammacin Kogi, waɗanda aka biya su haraji, da kuɗin shiga da fita na kaya, da kuɗin fito.


Sai Sulemanu ya tafi ya ci Hamat-zoba da yaƙi.


Ka sa ƙasar ta girgiza, ka tsaga ta. Yanzu sai ka warkar da tsaguwarta, gama tana gab da fāɗuwa!


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ