Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 18:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Da haka Dawuda ya yi mulki bisa dukan Isra'ila. Ya yi wa dukan jama'arsa adalci da gaskiya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Dawuda ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila, yana yin abin da yake daidai da kuma gaskiya saboda dukan mutanensa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 18:14
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A waɗannan kwanaki da a lokacin nan, zan sa wani reshe mai adalci ya fito daga zuriyar Dawuda, zai aikata gaskiya da adalci a ƙasar.


A gaskiya da adalci aka kafa mulkinka, Akwai ƙauna da aminci a dukan abin da kake yi.


Kana tsammani kai sarki ne, Da yake ƙasarka ta itacen al'ul ce? Amma ubanka ya ci, ya sha, Ya yi gaskiya, ya aikata adalci, Ya kuwa zauna lafiya.


Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin, Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa, Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.


Duk waɗannan mayaƙa sun zo Hebron a shirye, da zuciya ɗaya don su naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila duka. Haka kuma dukan sauran Isra'ilawa suka goyi baya da zuciya ɗaya a naɗa Dawuda ya zama sarki.


Dawuda ya mallaki Isra'ila duka. Ya yi wa dukan jama'arsa shari'ar gaskiya da adalci.


Sai ya sa ƙungiyoyin sojoji a Edom, dukan Edomawa kuma suka zama bayin Dawuda. Ubangiji kuwa ya taimaki Dawuda duk inda ya tafi.


Yowab ɗan Zeruya shi ne shugaban sojoji, Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubuci.


Dawuda ɗan Yesse ya yi mulki bisa dukan Isra'ila,


Ka koya wa sarki ya yi shari'a Da adalcinka, ya Allah, Ka kuma ba shi shari'arka,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ