1 Tarihi 18:11 - Littafi Mai Tsarki11 Sarki Dawuda kuwa ya keɓe waɗannan ga Ubangiji, tare da azurfa da zinariya waɗanda ya kwaso daga al'umman da ya ci, wato Edom, da Mowab, da mutanen Ammon, da na Filistiya, da na Amalek. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202011 Sarki Dawuda ya miƙa waɗannan kayayyakin ga Ubangiji, kamar yadda ya yi da azurfa da kuma zinariyan da ya kwaso daga dukan waɗannan al’ummai. Edom da Mowab, Ammonawa da Filistiyawa, da kuma Amalek. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Da wahala mai yawa na yi tanadi domin Haikalin Ubangiji, zinariya wajen talanti dubu ɗari (100,000), da azurfa kuma wajen talanti zambar dubu (1,000,000), domin gina Haikalin Ubangiji. Bayan wannan akwai tagulla da ƙarfe masu tarin yawa. Na kuma tanada katakai da duwatsu. Kai kuma sai ka ƙara a kansu.
Sai Yowash Sarkin Yahuza ya kwashe dukan kyautai na yardar rai waɗanda Yehoshafat, da Yoram, da Ahaziya, kakanninsa, sarakunan Yahuza suka keɓe, ya kuma kwashe kyauta ta yardar rai ta kansa, da dukan zinariya da aka samu a baitulmalin Haikalin Ubangiji da baitulmalin gidan sarki, ya aika wa Hazayel, Sarkin Suriya. Sa'an nan Hazayel ya tashi ya bar Urushalima.