1 Tarihi 18:10 - Littafi Mai Tsarki10 sai ya aiki Adoniram ɗansa wurin sarki Dawuda, don ya gaishe shi, ya kuma yabe shi saboda ya yi yaƙi da Hadadezer, har ya ci shi, gama Hadadezer yakan yi yaƙi da Toyi. Adoniram kuwa ya kawo kayayyaki iri iri na zinariya, da na azurfa, da na tagulla. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 sai ya aiki ɗansa Hadoram zuwa wurin Sarki Dawuda yă gaishe shi yă kuma yi masa barka da nasara a yaƙi a kan Hadadezer, wanda yake yaƙi da Towu. Hadoram ya kawo kowane irin kayayyakin zinariya da na azurfa da na tagulla. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da Sarauniyar Sheba ta ji labarin irin suna da Sulemanu ya yi, sai ta zo Urushalima don ta jarraba shi da tambayoyi masu wuya. Ta zo da 'yan rakiya masu yawa, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, da zinariya mai yawa, da duwatsu masu daraja. Sa'ad da ta zo wurin Sulemanu, ta faɗa masa dukan abin da yake a ranta.