Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 17:6 - Littafi Mai Tsarki

6 A dukan wuraren da na tafi tare da Isra'ilawa, ban taɓa faɗa wa wani daga cikin hakiman Isra'ila, waɗanda na ba da umarni su yi kiwon jama'ata, cewa su gina mini ɗaki da itacen al'ul ba.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Duk inda na tafi tare da Isra’ilawa, na taɓa ce wa wani daga cikin shugabanninsu waɗanda na umarta su yi kiwon mutanena, “Don me ba ku gida mini gidan al’ul ba?” ’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 17:6
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A cikin kai da kawowata tare da dukan jama'ar Isra'ila ban taɓa ce wa wani daga cikin shugabannin Isra'ila waɗanda na sa su lura da jama'ata Isra'ila, ya gina mini ɗaki na katakon al'ul ba.’


“Sai ka rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Afisa haka, ‘Ga maganar wadda take riƙe da taurarin nan bakwai a hannunsa na dama, wadda kuma take tafiya a tsakiyar fitilun nan bakwai na zinariya.


Wace yarjejeniya ce take a tsakanin Haikalin Allah da gumaka? Domin mu haikali ne na Allah Rayayye. Yadda Allah ya ce, “Zan zauna tare da su, in yi yawo a tsakaninsu, Zan kuma kasance Allahnsu, Su kuma su kasance jama'ata.


Bayan haka kuma ya naɗa musu mahukunta har ya zuwa zamanin Annabi Sama'ila.


“ ‘Ke ma Baitalami, ta kasar Yahuza, Ko kusa ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin manyan garuruwan Yahuza ba, Domin daga cikinki za a haifi wani mai mulki, Wanda zai zama makiyayin jama'ata, Isra'ila.’ ”


Shi kuwa zai tashi ya ciyar da garkensa da ƙarfin Ubangiji, Da ɗaukakar sunan Ubangiji Allahnsa. Za su kuwa zauna lafiya, Gama zai zama mai girma cikin duniya duka.


“Ɗan mutum, ka yi annabci a kan makiyayan Isra'ila, ka ce musu, ‘Ku masu kiwon mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah na ce, kaito, kaito, ku masu kiwon mutanen Isra'ila, kuna kiwon kanku kawai! Ashe, ba makiyaya ne suke kiwon tumaki ba?


Zan sa makiyayan da za su lura da su. Ba kuwa za su ƙara jin tsoro, ko razana ba, ba kuma wanda zai ɓace, ni Ubangiji na faɗa.


Ko dā can lokacin da Saul yake sarauta, kai ne kake yi wa Isra'ilawa jagora zuwa yaƙi da komowa. Ubangiji Allahnka kuwa ya ce maka, ‘Za ka yi kiwon jama'ata, wato Isra'ilawa, ka kuma shugabance su.’ ”


Ubangiji kuwa ya aika musu da Yerubba'al, wato Gidiyon, da Barak, da Yefta, da Samson, suka cece ku daga hannun abokan gābanku ta kowace fuska. Sa'an nan kuka yi zamanku lafiya.


Gama Ubangiji Allahnku yakan yi yawo cikin sansaninku don ya cece ku, ya ba da magabtanku cikin hannunku. Saboda haka dole ku tsabtace sansaninku don kada Ubangiji ya iske wata ƙazanta a cikinku, ya rabu da ku.”


“Saboda haka fa sai ka faɗa wa bawana Dawuda cewa, ‘Ni Ubangiji Mai Runduna, na ɗauko ka daga kiwon tumaki domin ka zama sarkin jama'ata Isra'ila.


‘Tun daga ran da na fito da mutanena Isra'ila, daga Masar, ban zaɓi wani birni daga cikin kabilan Isra'ila inda zan gina Haikali domin sunana ba, amma na zaɓi Dawuda ya shugabanci mutanena Isra'ilawa.’ ”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ