15 Natan kuwa ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Allah ya bayyana masa.
15 Natan ya faɗa wa Dawuda dukan kalmomin wahayin nan.
domin ban ji nauyin sanar da ku dukan nufin Allah ba.
Bari annabin da yake da mafarki ya faɗi mafarkinsa, amma wanda yake da maganata ya faɗe ta da aminci. Me ya haɗa ciyawa da alkama? Ni Ubangiji na faɗa.
Haka kuwa Natan ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Allah ya bayyana masa.
Zan zauna da shi a gidana da mulkina har abada. Gadon sarautarsa kuwa zai kahu har abada.’ ”
Sarki Dawuda kuwa ya shiga alfarwa, ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Allah, mene kuma gidana da za ka yi mini haka?