A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.
Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin, Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa, Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.
Ubangiji kuma ya yi wa tsohona Dawuda alkawari ya ce, ‘Ɗanka, wanda zai gāje ka, shi zai gina mini Haikali.’ Yanzu kuwa na yi niyyar gina wannan haikali domin sujada ga Ubangiji Allahna.
Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”
To, sai suka ce mana, ‘Mu bayin Allah ne wanda yake da sama da ƙasa, muna sāke gina Haikalin da wani babban sarki na Isra'ila ya gina tun shekaru da yawa da suka wuce.
Ni zan zama uba a gare shi, shi kuwa ya zama ɗa a gare ni, ba zan kawar masa da madawwamiyar ƙaunata ba, kamar yadda na kawar da ita daga wanda ya riga ka sarauta.
Da ma a yi ta tunawa da sunansa har abada, Da ma shahararsa ta ɗore muddin rana tana haskakawa. Da ma dukan sauran al'umma su yabi sarkin, Dukan jama'a su roƙi Allah yă sa musu albarka, Kamar yadda ya sa wa sarki albarka.