1 Tarihi 16:40 - Littafi Mai Tsarki40 Kowace safiya da maraice suna miƙa hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a bisa bagaden ƙona hadaya, kamar yadda aka rubuta a dokokin Ubangiji, waɗanda ya ba Isra'ilawa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202040 don su miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden hadaya ta ƙonawa kullum, da safe da kuma yamma, bisa ga kome da yake a rubutacce a cikin Dokar Ubangiji, da ya ba wa Isra’ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga shi dai, na yi niyyar gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe masa shi, domin a riƙa ƙona masa turare mai daɗin ƙanshi, inda kuma za a riƙa ajiye gurasar ajiyewa dukan lokaci, don kuma a riƙa miƙa hadayun ƙonawa safe da yamma, da ranakun Asabar, da na amarya wata, da kuma a lokatan ƙayyadaddun idodin Ubangiji Allahnmu, yadda dai aka faralta a riƙa yi a cikin Isra'ila.