Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 16:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ya kuma rarraba wa Isra'ilawa mata da maza, gurasa, da gunduwar nama, da kauɗar zabibi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Sa’an nan ya ba da dunƙulen burodi da wainar dabino da kuma kauɗar zabibi ga kowane mutumin Isra’ila namiji da ta mace.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 16:3
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sarki ne da nawayar ba da hadayun ƙonawa, da na gari, da na sha a lokacin idodi da na amaryar wata, da ranakun Asabar, da lokacin dukan ƙayyadaddun idodin mutanen Isra'ila. Zai kuma ba da hadayu don zunubi da na salama domin a yi wa mutanen Isra'ila kafara.”


Sa'an nan ya ce musu, “Ku koma gidajenku ku ci abinci mai kyau, ku sha ruwan inabi mai zaƙi, ku kuma aika wa wanda ba shi da shi, gama wannan rana tsattsarka ce ta Ubangijinmu. Kada ku yi baƙin ciki, gama farin cikin da Ubangiji ya ba ku shi ne ƙarfinku.”


Ku riƙa yi wa juna baƙunta, ba tare da ƙunƙuni ba.


Gama Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya ba taron bijimai dubu (1,000) da tumaki dubu bakwai (7,000), don yin hadayu, sarakuna kuma sun ba taron bijimai dubu (1,000) da tumaki dubu goma (10,000). Firistoci da yawa suka tsarkake kansu.


Da Dawuda ya gama miƙa hadayar ƙonawa da ta salama, sai ya sa wa jama'a albarka da sunan Ubangiji.


Ya kuma sa waɗansu Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka Ubangiji Allah na Isra'ila, su gode masa, su kuma yabe shi.


Ka ciyar da ni da wainar zabibi, Ka ba ni 'ya'yan gawasa in sha in wartsake! Gama na cika da sha'awarka.


Mutanen Mowab za su yi kuka saboda wahalar da suke sha. Dukansu za su yi kuka sa'ad da suka tuna da kyakkyawan abincin da suka riƙa ci a birnin Kir-hareset. Za a kore su har su fid da zuciya.


Ubangiji kuma ya ce mini, “Ka sāke tafiya, ka ƙaunaci karuwa wadda take tare da kwartonta. Ka ƙaunace ta kamar yadda ni Ubangiji nake ƙaunar mutanen Isra'ila, ko da yake suna bin gumaka, suna ƙaunar wainar zabibi da aka miƙa wa gumaka.”


Da Sulemanu ya farka, ashe, mafarki ne, Sa'an nan ya zo Urushalima, ya tafi ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Ya miƙa hadayu na ƙonawa, da hadayu na salama. Ya kuma yi wa dukan barorinsa biki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ