Da ba domin Allah na mahaifina da Ibrahim, da martabar Ishaku na wajena ba, hakika da yanzu ka sallame ni hannu wofi. Allah ya ga wahalata da aikin hannuwana, ya kuwa tsauta maka a daren jiya.”
Ina da iko in yi maka lahani, amma Allah na mahaifinka, ya yi magana da ni a daren jiya, yana cewa, ‘Ka kula fa kada ka ce wa Yakubu kome, ko nagari ko mugu.’