18 “Zan ba ka ƙasar Kan'ana, Za ta zama mallakarka.”
18 “Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana kamar rabon da za ka gāda.”
gama dukan ƙasan nan da kake gani kai zan ba, da zuriyarka har abada.
Don haka ba za ku sami wanda zai sa muku ma'auni A taron jama'ar Ubangiji ba.
Sa'ad da Maɗaukaki ya ba al'ummai gādonsu, Sa'ad da ya raba 'yan adam, Ya yanka wa mutane wurin zama bisa ga yawan Isra'ilawa.
Zan ba ka, kai da zuriyarka a bayanka, ƙasar baƙuncinka, wato dukan ƙasar Kan'ana ta zama mallakarka har abada, ni kuwa zan zama Allahnsu.”
Sai Ubangiji ya bayyana ga Abram, ya ce, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa.” Sai ya gina bagade ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi.
Jama'ar Ubangiji kima ne, Baƙi ne kuwa a ƙasar.