Ka yi baƙunci cikin wannan ƙasa, ni kuwa zan kasance tare da kai, zan sa maka albarka, gama a gare ka da zuriyarka ne na ba da waɗannan ƙasashe, zan kuwa cika rantsuwar da na yi wa Ibrahim mahaifinka.
Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka hayayyafa ka riɓaɓɓanya, al'umma da tattaruwar al'ummai za su bumbunto daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga cikinka.
A wannan rana Ubangiji ya yi wa Abram alkawari ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga Kogin Masar zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis ke nan,
Ku ne tsatson annabawa, ku ne kuma magadan alkawarin da Allah ya yi wa kakanninku, da ya ce wa Ibrahim, ‘Ta zuriyarka ne za a yi wa dukkan kabilan duniya albarka.’
Ka iske shi amintacce a gare ka, Ka kuwa yi masa alkawari. Ka yi alkawari za ka ba shi ƙasar Kan'ana, Da ta Hittiyawa, da ta Amoriyawa, da ta Ferizziyawa, Da ta Yebusiyawa, da ta Girgashiyawa, Ta zama inda zuriyarsa za su zauna. Ka kuwa cika alkawarinka, gama kai mai aminci ne.
Allah kuma ya sāke ce wa Musa, “Faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Ubangiji Allah na kakanninku, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu ya aiko ni gare ku.’ Wannan shi ne sunana har abada. Da wannan suna za a tuna da ni a dukkan zamanai.
Amma saboda Ubangiji ya ƙaunace ku, yana kuma so ya cika rantsuwar da ya yi wa kakanninku, shi ya sa ya fisshe ku da dantse mai iko ya fanshe ku kuma daga gidan bauta, wato daga ikon Fir'auna, Sarkin Masar.
Aka faɗa wa Dawuda sarki, cewa, Ubangiji ya sa wa gidan Obed-edom albarka, da dukan abin da yake da shi saboda akwatin alkawarin Allah. Sai Dawuda ya tafi da murna ya kawo akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-edom zuwa Birnin Dawuda.