Ku tafi wurin Ubangiji ku tsira. Idan kuwa kun ƙi, Shi zai babbaka jama'ar Yusufu Kamar yadda a kan babbaka da wuta. Wuta za ta ƙone jama'ar Betel, Ba kuwa mai kashe wutar.
Yanzu fa, ya Ubangiji ka tashi ka tafi wurin hutawarka, kai da akwatin ikonka. Ya Ubangiji Allah ka yi wa firistocinka sutura da cetonka, adalanka kuma su yi farin ciki da nagartarka.