Kwana guda da za a yi a Haikalinka, Ya fi kwana dubu da za a yi a wani wuri dabam. Na gwammace in tsaya a ƙofar Haikalin Allahna, Da in zauna a gidajen mugaye.
Sai suka tafi wurin masu gadin ƙofar birnin, suka ce musu, “Mun tafi sansanin Suriyawa ba mu ga kowa ba, ba mu kuma ji motsin kowa a wurin ba, ba kowa a wurin sai dawakai da jakai, a ɗaure, alfarwai kuma suna nan yadda suke.”
Sai Shebaniya, da Yehoshafat, da Netanel, da Amasai, da Zakariya, da Benaiya, da Eliyezer, firistoci, suka yi ta busa ƙaho a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-edom da Yehiya su ne kuma masu tsaron ƙofar akwatin alkawari.