1 Tarihi 15:2 - Littafi Mai Tsarki2 Sai Dawuda ya ce, “Kada wani ya ɗauki akwatin alkawari na Allah sai Lawiyawa kaɗai, gama su ne Ubangiji ya zaɓa domin su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, su kuma yi masa hidima har abada.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 Sa’an nan Dawuda ya ce, “Babu wani sai ko Lawiyawa kaɗai za su ɗauka akwatin alkawarin Allah, gama Ubangiji ya zaɓe su su ɗauka akwatin alkawarin Ubangiji su kuma yi hidima a gabansa har abada.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ya kuma faɗa wa Lawiyawa, tsarkakakku na Ubangiji, waɗanda suke koya wa dukan Isra'ila, ya ce, “Ku sa tsattsarkan akwatin alkawari a Haikalin da Sulemanu ɗan Dawuda, Sarkin Isra'ila, ya gina. Ba za ku sāke ɗaukarsa bisa kafaɗunku ba. Yanzu fa sai ku kama hidimar Ubangiji Allahnku da jama'arsa Isra'ila.