Wata rana sai uku daga cikin manyan mutanen nan talatin suka gangara zuwa dutsen Dawuda, a kogon Adullam, sa'ad da rundunar sojojin Filistiyawa suka kafa sansani a kwarin Refayawa.
Isra'ila za ta zama kamar gonar da aka girbe, aka yanke amfaninta, ta zama marar kome kamar gona a kwarin Refayawa sa'ad da aka ɗebe amfaninta. Mutane kima ne kurum za su ragu.
Sai jarumawa uku daga cikin jarumawa talatin, suka tafi wurin Dawuda a kogon Adullam, gab da lokacin girbi. A lokacin kuwa Filistiyawa sun kafa sansani a kwarin Refayawa.
Sa'ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila duka, sai dukan Filistiyawa suka haura, suna neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya fita domin ya yi yaƙi da su.
Sai Dawuda ya roƙi Allah, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Filistiyawa? Za ka bashe su a hannuna?” Ubangiji kuwa ya amsa masa, ya ce, “Ka haura, gama zan bashe su a hannunka.”