Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 13:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Sai Dawuda tare da dukan Isra'ilawa, suka haura zuwa Ba'al, wato Kiriyat-yeyarim ta Yahuza, domin su ɗauko akwatin alkawarin Allah daga can, inda ake kira bisa sunan Ubangiji, wanda kuma yake zaune a wurin kerubobi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Dawuda da dukan Isra’ilawa tare da shi suka tafi Ba’ala na Yahuda (Kiriyat Yeyarim) don su haura daga can su kawo akwatin alkawarin Allah Ubangiji, wanda yake zama tsakanin kerubobi, akwatin alkawarin da ake kira da Sunan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 13:6
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta kuma milla daga kan dutsen zuwa maɓuɓɓugar ruwan Neftowa, daga can zuwa biranen Dutsen Efron. Daga can kuma ta karkata zuwa Ba'ala, wato Kiriyat-yeyarim.


Sa'an nan ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, kai da kake zaune a kan gadon sarautarka, kai kaɗai ne Allah a dukan mulkokin duniya, kai ne ka yi sama da ƙasa.


A nan zan zo in sadu da kai, in yi magana da kai, wato tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari. Zan ba ka umarnaina duka don Isra'ilawa.”


Sai suka aika zuwa Shilo aka kawo akwatin alkawarin Ubangiji Mai Runduna, wanda yake zaune a tsakanin kerubobi. 'Ya'yan nan na Eli, maza guda biyu, wato Hofni da Finehas, suna tare da akwatin alkawarin.


Da kuma Kiriyat-ba'al, wato Kiriyat-yeyarim, da Rabba, birane biyu ke nan da ƙauyukansu.


ya ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, kana kan kursiyinka, kai kaɗai ne Allah, kana mulkin dukan mulkokin duniya. Ka halicci duniya da sararin sama.


Ubangiji Sarki ne, Mutane suna rawar jiki, Yana zaune a bisa kursiyinsa a bisa kerubobi, Duniya ta girgiza.


Ka kasa kunne gare mu, ya Makiyayin Isra'ila, Ka ji mu, kai da kake shugaban garkenka, Da kake zaune a kan kursiyinka, a bisa kerubobi.


‘Tun daga ran da na fito da mutanena Isra'ila, daga Masar, ban zaɓi wani birni daga cikin kabilan Isra'ila inda zan gina Haikali domin sunana ba, amma na zaɓi Dawuda ya shugabanci mutanena Isra'ilawa.’ ”


Duk lokacin da Musa ya shiga alfarwa ta sujada domin ya yi magana da Ubangiji, sai ya ji Ubangiji yana magana da shi daga bisa murfin akwatin alkawari, a tsakanin kerubobi masu fikafikai biyu.


Idan suka sa wa jama'a wannan albarka sa'ad da suke addu'a ga Ubangiji domin Isra'ilawa, Ubangiji zai sa musu albarka.


Ku nuna masa bangirma, ku kasa kunne ga maganarsa. Kada ku tayar masa, gama ba zai gafarta muku laifofinku ba, gama shi wakilina ne.


Za ku gina mini bagade na ƙasa. A kansa za ku miƙa mini hadayu na ƙonawa da na salama, da tumakinku da shanunku. A duk inda na sa a tuna da sunana zan zo wurinku in sa muku albarka.


Sai Isra'ilawa suka kama hanyarsu a rana ta uku suka isa biranen mutanen, wato Gibeyon, da Kefira, da Biyerot, da Kiriyat-yeyarim.


Sai suka aiki manzanni wurin mutanen Kiriyat-yeyarim, suka ce, “Filistiyawa sun komo da akwatin alkawari na Ubangiji, sai ku zo, ku ɗauka, ku tafi da shi.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ