Esta kuwa ta miƙe tsaye a gaban sarki, ta ce, “Idan sarki ya yarda, idan kuma na sami tagomashi a wurinka, idan ya yi wa sarki kyau, idan kuma sarki yana jin daɗina, bari a yi rubutu a soke wasiƙun da Haman Ba'agage ɗan Hammedata ya rubuta don a hallaka Yahudawan da suke cikin dukan lardunan sarki.
Haka fa, Dawuda ya tattara dukan Isra'ilawa wuri ɗaya, daga Shihor ta Masar, har zuwa mashigin Hamat domin a kawo akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim.