1 Tarihi 13:3 - Littafi Mai Tsarki3 Sa'an nan mu ɗauko akwatin alkawari na Allahnmu mu kawo shi wurinmu, gama mun ƙyale shi tun zamanin Saul.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Bari mu ɗauko akwatin alkawarin Allahnmu mu kawo wurinmu, gama ba mu neme shi a lokacin mulkin Shawulu ba.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ya kuma yi magana da dukan taron Isra'ilawa, ya ce, “Idan kun ga ya yi kyau, idan kuma nufin Ubangiji Allahnmu ne, to, bari mu aika a ko'ina wurin 'yan'uwanmu waɗanda aka rage a ƙasar Isra'ila, mu kuma aika wa firistoci da Lawiyawa waɗanda suke tare da su a biranensu masu makiyaya domin su zo wurinmu.