1 Tarihi 13:1 - Littafi Mai Tsarki1 Sa'an nan Dawuda ya yi shawara da shugabannin sojoji na dubu dubu da na ɗari ɗari, da kowane shugaba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 Sai Dawuda ya tattauna da kowane ɗaya daga cikin shugabanninsa, shugabannin sojoji na dubu-dubu da na ɗari-ɗari. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗanda kuma suke kusa da su har zuwa Issaka, da Zabaluna da Naftali, sun kawo abinci a kan jakuna, da raƙuma, da alfadarai, da takarkarai. Suka kawo abinci mai yawa, wato gāri da kauɗar ɓaure da nonnan busassun 'ya'yan inabi, da ruwan inabi, da man zaitun. Suka kuma kawo shanu da tumaki domin yanka a ci. Duk an yi wannan domin a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra'ila.
Ya kuma yi magana da dukan taron Isra'ilawa, ya ce, “Idan kun ga ya yi kyau, idan kuma nufin Ubangiji Allahnmu ne, to, bari mu aika a ko'ina wurin 'yan'uwanmu waɗanda aka rage a ƙasar Isra'ila, mu kuma aika wa firistoci da Lawiyawa waɗanda suke tare da su a biranensu masu makiyaya domin su zo wurinmu.