1 Tarihi 12:8 - Littafi Mai Tsarki8 Waɗannan su ne sunayen shahararru, ƙwararrun mayaƙa daga kabilar Gad, waɗanda suka haɗa kai da sojojin Dawuda, sa'ad da yake a kagara a hamada. Su gwanayen yaƙi da garkuwa da mashi ne. Fuskokinsu kamar na zakoki, saurinsu kamar bareyi a kan dutse. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Sai waɗansu mutanen Gad suka koma suna goyon bayan Dawuda suka kuma haɗa kai da shi a kagararsa a hamada. Su ƙwararrun mayaƙa ne, a shirye don yaƙi, kuma suna iya riƙe garkuwa da māshi. Fuskokinsu kamar fuskoki zakoki, kuma suna da sauri kamar bareyi a kan duwatsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan Amaziya ya tattara mazajen Yahuza, ya kasa su bisa ga gidajen kakanninsu, a ƙarƙashin shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, a dukan Yahuza da Biliyaminu. Sai ya tara 'yan shekara ashirin ko fi, ya sami mutum dubu ɗari uku (300,000) ƙarfafa, waɗanda suka isa zuwa yaƙi, wato za su iya riƙon māshi da garkuwa.