1 Tarihi 12:39 - Littafi Mai Tsarki39 Suka yi kwana uku tare da Dawuda, suka yi ta ci suna sha, gama 'yan garin sun shirya wata liyafa dominsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202039 Mutanen suka yi kwana uku a can tare da Dawuda, suna ci suna sha, gama iyalansu sun yi musu tanadi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗanda kuma suke kusa da su har zuwa Issaka, da Zabaluna da Naftali, sun kawo abinci a kan jakuna, da raƙuma, da alfadarai, da takarkarai. Suka kawo abinci mai yawa, wato gāri da kauɗar ɓaure da nonnan busassun 'ya'yan inabi, da ruwan inabi, da man zaitun. Suka kuma kawo shanu da tumaki domin yanka a ci. Duk an yi wannan domin a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra'ila.