1 Tarihi 12:20 - Littafi Mai Tsarki20 Sa'ad da yake komawa Ziklag sai sojojin Manassa suka zo wurinsa, wato su Adana, da Yozabad, da Yediyayel, da Maikel, da Yozabad, da Elihu, da Zilletai. A sojojin kabilar Manassa, waɗannan shugabannin sojoji ne na dubu dubu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202020 Da Dawuda ya tafi Ziklag, waɗannan mutanen Manasse ne suka haɗa kai da shi. Adna, Yozabad, Yediyayel, Mika’ilu, Yozabad, Elihu da Zilletai, shugabannin ƙungiyoyi na dubu a cikin Manasse. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗansu sojoji daga Manassa, suka tafi wurin Dawuda sa'ad da yake fita tare da Filistiyawa don su yi yaƙi da Saul. Amma Dawuda bai tafi tare da su ba, domin sarakunan Filistiyawa sun yi shawara, suka sallame shi, don kada ya juya musu gindin baka, ya nemi sulhu a wurin shugabansu Saul, da kawunansu.