1 Tarihi 12:17 - Littafi Mai Tsarki17 Sai Dawuda ya fito don ya tarye su, ya ce musu, “Idan da salama kuka zo wurina don ku taimake ni, to, zuciyata za ta zama ɗaya da taku, amma idan kun zo ne don ku bashe ni ga maƙiyana, to, Allah na kakanninmu ya duba ya shara'anta, da yake ba ni da laifi.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202017 Sai Dawuda ya fita don yă tarye su, ya kuma ce musu, “In kun zo wurina da salama, don ku taimake ni, to, ina a shirye in bar ku ku haɗa kai tare da ni. Amma in kun zo don ku bashe ni ga abokan gābana sa’ad da hannuwana ba su da laifi a rikici, bari Allah na kakanninmu yă duba yă kuma shari’anta ku.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Da ya tashi daga can, sai ya sadu da Yehonadab ɗan Rekab yana zuwa ya tarye shi. Yehu ya gaishe shi, ya tambaye shi, “Zuciyarka ta amince da ni kamar yadda tawa ta amince da kai?” Yehonadab ya amsa, “I.” Sai Yehu ya ce, “Idan haka ne, to, miƙo mini hannunka.” Sai ya miƙa masa hannunsa. Yehu kuwa ya ɗauke shi zuwa cikin karusa.