7 Sa'an nan Dawuda ya zauna a kagara, don haka aka kira birnin, birnin Dawuda.
7 Dawuda zauna a kagarar, ta haka aka kira ta Birnin Dawuda.
Ya ce, “A bisa Sihiyona, dutsena tsattsarka, Na naɗa sarkina.”
Sai mazaunan Yebus, suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba.” Duk da haka Dawuda ya ci Sihiyona, gari mai kagara, wato birnin Dawuda ke nan.
Duk da haka Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, wato birnin Dawuda.
Sai Dawuda ya ce, “Duk wanda ya ci Yebusiyawa da fari shi ne zai zama babban shugaban sojoji.” Yowab ɗan Zeruya ne ya fara tafiya, domin wannan aka maishe shi shugaba.
Sai ya rutsa birnin da gini tun daga Millo. Yowab kuma ya gyaggyara sauran birnin.