Sa'ad da ka isa Gibeya, wato tudun Allah, inda sansanin sojojin Filistiyawa yake, a nan kuma sa'ad da kake shiga garin, za ka tarar da ƙungiyar annabawa suna gangarowa daga wurin bagaden a kan tudu suna kaɗa garaya, da kuwaru, da sarewa, da molo, suna rawa suna sowa.
Isra'ilawa duka kuwa suka ji wai Saul ya kashe shugaban yaƙi na Filistiyawa, da kuma, Isra'ilawa sun zama abin ƙi ga Filistiyawa, sai jama'a suka amsa kiran, suka tafi wurin Saul a Gilgal.
Saul da mutanensa suka tafi neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya sauka daga dutsen ya zauna a can jejin Mawon. Da Saul ya ji, sai ya bi Dawuda zuwa jejin Mawon.
Sa'ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila, sai dukansu suka haura zuwa neman ran Dawuda. Da Dawuda ya ji Filistiyawa suna nemansa, sai ya gangara zuwa kagara.