Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 10:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Sai Saul ya ce wa mai ɗaukar makamansa, “Zare takobinka, ka kashe ni, don kada marasa kaciyan nan su zo su yi mini ba'a.” Amma mai ɗaukar makamai nasa bai yarda ba, gama yana jin tsoro ƙwarai. Saboda haka sai Saul ya zare takobinsa ya fāɗi a kansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Sai Shawulu ya ce wa mai riƙe masa kayan yaƙi, “Zare takobinka ka soke ni, in ba haka ba waɗannan marasa kaciya za su zo su yi mini ba’a.” Amma mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ji tsoro bai kuwa yi haka ba; saboda haka Shawulu ya zāre takobinsa ya fāɗi a kansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 10:4
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ya ce wa mai ɗaukar masa makamai, “Ka zare takobinka ka sha zarata da shi domin kada marasa kaciyan nan su zo su sha zarata, su yi mini ba'a.” Amma mai ɗaukar masa makamai bai yarda ba, domin ya ji tsoro da yawa. Sai Saul ya zare takobinsa, ya faɗa a kansa.


Da yāri ya farka daga barci ya ga ƙofofin kurkuku a buɗe, ya zaro takobinsa, yana shirin kashe kansa, cewa yake 'yan sarƙa sun gudu.


(To, shi mutumin nan, da ladan mugun aikinsa ya sayi wani fili, sai ya fāɗi da kā, cikinsa ya fashe, kayan cikinsa duk suka zubo.


Sa'ad da mai ɗaukar makamansa ya ga Saul ya mutu, sai shi ma ya faɗi a kan takobinsa ya mutu.


Da Zimri ya ga an ci birnin, sai ya tafi ya shiga hasumiyar da take a fāda, ya sa wa fādar wuta, wutar kuwa ta ƙone shi ya mutu.


Da Ahitofel ya ga ba a bi shawararsa ba, sai ya yi wa jakinsa shimfiɗa ya hau, ya koma garinsu. Da ya kintsa gidansa, sai ya rataye kansa, ya mutu, aka binne shi a kabarin mahaifinsa.


Kada a ba da labarin a Gat, Ko a titin Ashkelon. Kada ku sa matan Filistiyawa su yi murna, Kada ku sa 'yan matan arna su yi farin ciki.


Baranka ya taɓa kashe zaki da beyar, wannan arne zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, tun da yake ya raina rundunar Allah mai rai.


Sai Dawuda ya tambayi mutanen da suke kusa da shi, ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilisten nan, har ya kawar da zargi daga Isra'ila? Gama wane ne wannan Bafiliste, marar kaciya, da zai raina rundunar Allah mai rai?”


Jonatan ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye zuwa sansanin marasa kaciyan nan, arnan nan, watakila Ubangiji zai yi aiki ta wurinmu, gama ba abin da zai hana Ubangiji ya yiwo ceto ta wurin masu yawa, ko kuwa ta wurin 'yan kaɗan.”


Filistiyawa fa suka kama shi, suka ƙwaƙule idanunsa, suka gangara da shi zuwa Gaza. Suka ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla. Ya yi ta niƙa a kurkuku.


Ƙishirwa kuwa ta kama shi ƙwarai, sai ya roƙi Ubangiji ya ce, “Kai ne ka yi wannan babbar nasara ta hannun bawanka, yanzu kuwa ko zan mutu da ƙishirwa, har Filistiyawa marasa kaciya su kama ni?”


Nan da nan sai Abimelek ya kira saurayin da yake ɗaukar masa makamai, ya ce masa, “Ka zaro takobinka, ka kashe ni domin kada mutane su ce, ‘Mace ta kashe shi.’ ” Sai saurayin ya soki Abimelek, ya mutu.


Mutumin kuwa ya amsa ya ce, “Ya zama fa ina kan dutsen Gilbowa, sai ga Saul ya jingina a māshinsa. Karusai da mahayan dawakan abokan gāba sun rutsa shi.


Yaƙin ya tsananta wa Saul, maharba suka rutsa Saul, suka yi masa rauni.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ