Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 10:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Filistiyawa suka kama Saul da 'ya'yansa maza, suka kashe Jonatan da Yishwi, da Malkishuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Filistiyawa suka matsa sosai suna bin Shawulu da ’ya’yansa maza, suka kuma kashe ’ya’yansa maza Yonatan, Abinadab da Malki-Shuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 10:2
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ner ya haifi Kish, Kish kuma ya haifi Saul, Saul ya haifi Jonatan, da Malkishuwa, da Yishwi, da Ish-boshet.


Ner shi ne mahaifin Kish, Kish kuma shi ne mahaifin Saul, Saul shi ne mahaifin Jonatan, da Malkishuwa, da Yishwi, da Ish-boshet.


Aka kashe 'ya'yansa maza a idonsa, sa'an nan aka ƙwaƙule masa idanu, aka kuma ɗaure shi da sarƙa, aka kai shi Babila.


A zamaninsa Fir'auna-neko, Sarkin Masar, ya tafi ya tasar wa Sarkin Assuriya da yaƙi a Kogin Yufiretis. Sarki Yosiya kuwa ya yi ƙoƙari ya hana shi wucewa, sa'ad da Fir'auna-neko ya gan shi, sai ya kashe shi a filin yaƙi a Magiddo.


'Ya'yan Saul, maza ke nan, Jonatan, da Yishwi, da Malkishuwa. Yana kuma da 'ya'ya mata biyu, Merab, 'yar fari, da Mikal.


Jonatan ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye zuwa sansanin marasa kaciyan nan, arnan nan, watakila Ubangiji zai yi aiki ta wurinmu, gama ba abin da zai hana Ubangiji ya yiwo ceto ta wurin masu yawa, ko kuwa ta wurin 'yan kaɗan.”


Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.


Filistiyawa suka ci Saul da 'ya'yansa maza. Suka kashe Jonatan, da Abinadab, da Malkishuwa, 'ya'yan Saul.


Yaƙin ya tsananta wa Saul, maharba suka rutsa Saul, suka yi masa rauni.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ