Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 1:32 - Littafi Mai Tsarki

32 'Ya'ya maza na Ketura, wato ƙwarƙwarar Ibrahim, su ne Zimran, da Yokshan, da Medan, da Madayana, da Yisbak, da Shuwa. 'Ya'yan Yokshan, maza, su ne Sheba, da Dedan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

32 ’Ya’yan Ketura maza, ƙwarƙwarar Ibrahim su ne, Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa. ’Ya’yan Yokshan maza su ne, Sheba da Dedan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 1:32
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta Edom. Zan kashe mutanenta da dabbobinta, zan maishe ta kufai. Za a kashe su da takobi, tun daga Teman har zuwa Dedan.


Ku mazaunan Dedan, ku juya, ku gudu, Ku ɓuya cikin zurfafa, Gama zan kawo masifa a kan Isuwa A lokacin da zan hukunta shi,


Babban ayarin raƙuma zai zo daga Madayana da Efa. Za su zo daga Sheba, su kawo zinariya da kayan ƙanshi. Mutane za su ba da labari mai daɗi a kan abin da Allah ya yi!


Wannan shi ne jawabi a kan Arabiya. Ya ku jama'ar Dedan, waɗanda ayarorinku suka yi zango a ƙasar Arabiya wadda take faƙo,


Ran sarki yă daɗe! Da ma a ba shi zinariya daga Arabiya, Da ma a yi masa addu'a dukan lokaci, Allah ya sa masa albarka kullum!


Sarakunan Esbanya da na tsibirai, Za su ba shi kyautai, Sarakunan Arabiya da na Habasha Za su kawo masa kyautai.


Ayari daga Sheba da Tema suka yi ta nema,


Sarauniyar Sheba ta ji labarin sunan da Sulemanu ya yi ta dalilin sunan Ubangiji, ta zo don ta jarraba shi da tambayoyi masu wuya.


“Ka ɗaukar wa Isra'ilawa fansa a kan Madayanawa. Bayan ka yi wannan za ka mutu.”


Sai ga wani Ba'isra'ile ya taho da wata mace, Bamadayaniya, ya kai ta alfarwarsa ƙiriƙiri a gaban Musa da dukan taron jama'ar Isra'ila a sa'ad da suke kuka a ƙofar alfarwa ta sujada.


Da Madayanawa, fatake, suna wucewa, sai suka jawo Yusufu suka fitar da shi daga cikin rijiyar suka sayar wa Isma'ilawa a bakin azurfa ashirin, aka kuwa tafi da Yusufu zuwa Masar.


da Yetur, da Nafish, da Kedema. Waɗannan su ne 'ya'yan Isma'ilu, maza.


'Ya'yan Madayana, maza, su ne Efa, da Efer, da Hanok, da Abida, da Eldaya. Waɗannan duka su ne 'ya'yan Ketura, maza.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ