27 Tera ya haifi Abram, wato Ibrahim ke nan.
27 da Abram (wato, Ibrahim).
Kai ne, ya Ubangiji Allah, ka zaɓi Abram, Ka fito da shi daga Ur ta Kaldiyawa, Ka sāke sunansa ya zama Ibrahim.
Joshuwa kuwa ya ce wa mutane duka, “Ga abin da Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘A zamanin dā kakanninku, su Tera, mahaifin Ibrahim, da Nahor, suna zaune a hayin Yufiretis. Suka bauta wa gumaka.
Ba za a ƙara kiran sunanka Abram ba, amma sunanka zai zama Ibrahim, gama na sa ka, ka zama uba ga al'ummai masu ɗumbun yawa.
Reyu ya haifi Serug, Serug ya haifi Nahor, Nahor ya haifi Tera,
'Ya'yan Ibrahim, maza, su ne Ishaku da Isma'ilu.