Sa'ad da dukan sarakunan da suke hayin Urdun, na cikin ƙasar tuddai, da na ƙasar kwari a gefen Bahar Rum har zuwa Lebanon, wato sarakunan Hittiyawa, da na Amoriyawa, da na Kan'aniyawa, da na Ferizziyawa, da na Hiwiyawa, da na Yebusiyawa, suka ji wannan labari,
Rifkatu kuwa ta ce wa Ishaku, “Na gaji da raina saboda matan Hittiyawa. Idan Yakubu zai auri ɗaya daga cikin waɗannan mata na Hittiyawa, wato daga matan ƙasar, wane amfani raina zai daɗa mini?”