Ubangiji ya ce, “Jama'ar Isra'ila, Ina yi da ku daidai yadda nake yi da Habashawa. Na fito da Filistiyawa daga Kaftor, Suriyawa kuwa daga Kir, Daidai yadda na fito da ku daga Masar.
Domin lokacin hallaka dukan Filistiyawa ya yi. Za a datse wa Taya da Sidon kowane taimakon da ya ragu, Gama Ubangiji zai hallaka Filistiyawa Waɗanda suke baƙin teku na Kaftor.
Haka nan kuma ya faru da Awwiyawa mazaunan ƙauyukan da suke kewaye da Gaza, wato su Kaftorawa waɗanda suka zo daga Kaftor, suka hallakar da su, suka zauna a wurinsu.)