Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 9:5 - Littafi Mai Tsarki

5 sa'an nan zan kafa gadon sarautarka a bisa Isra'ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa tsohonka, Dawuda, sa'ad da na ce masa ba za a rasa mutum daga zuriyarsa wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 zan kafa kujerar sarautarka a bisa Isra’ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani a kan kujerar sarautar Isra’ila ba.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 9:5
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

domin Ubangiji ya cika maganar da ya faɗa mini cewa, ‘Idan 'ya'yanka suna lura da hanyarsu, sun yi tafiya a gabana da gaskiya da zuciya ɗaya, da dukan ransu, ba za ka rasa mutum wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba.’


“Idan ka yi biyayya da dokokina da umarnaina, to, zan cika maka alkawarin da na yi wa tsohonka Dawuda.


Gidanka kuwa da mulkinka za su dawwama a gabana har abada. Gadon sarautarka kuma zai kahu har abada.’ ”


Sa'ad da kwanakinka suka ƙare, za ka rasu tare da kakanninka. A bayanka, zan ta da ɗanka, na cikinka. Zan sa mulkinsa ya kahu.


Yanzu Ubangiji ya cika alkawarin da ya yi, gama na tashi a maimakon tsohona, Dawuda, na hau gadon sarautar Isra'ila, kamar yadda ya alkawarta, ga shi kuwa, na gina Haikali saboda Ubangiji Allah na Isra'ila.


Ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na Isra'ila, wanda ya cika alkawarin da ya yi wa tsohona, Dawuda, da ya ce masa,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ