Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 9:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Amma kai, idan ka yi tafiya a gabana kamar yadda tsohonka, Dawuda, ya yi da aminci, da sahihanci, kana aikata dukan abin da na umarce ka, kana kuma kiyaye dokokina da ka'idodina,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 “Kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana da mutunci a zuci da kuma gaskiya, kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka yi dukan abin da na umarta, ka kuma yi biyayya da ƙa’idodina da kuma dokokina,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 9:4
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

domin Dawuda ya aikata abu mai kyau a gaban Ubangiji. Bai ƙetare umarnin da Ubangiji ya ba shi ba dukan kwanakin ransa, sai dai a kan Uriya Bahitte.


Idan za ka yi mini biyayya ka kuma kiyaye dokokina, da umarnaina kamar yadda tsohonka Dawuda ya yi, to, zan ba ka tsawon rai.”


Ya yi wa Ubangiji zunubi. Bai bi Ubangiji da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba.


sa'ad da Sulemanu ya tsufa sai suka janye zuciyarsa zuwa bin waɗansu gumaka, bai bi Ubangiji Allahnsa da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba.


A lokacin da Abram yake da shekara tasa'in da tara Ubangiji ya bayyana gare shi, ya ce masa, “Ni ne Allah Mai Iko Dukka. Ka yi mini biyayya, ka zama kamili.


Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna bin umarnin Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi.


“Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Idan ka yi tafiya a hanyata, ka kuma kiyaye umarnina, zan sa ka zama shugaban Haikalina, ka lura da shirayina, zan kuma sa ka sami damar zuwa wurin waɗannan da yake tsaye.


Ka yi aminci za ka zauna lafiya, idan kuwa ka yi rashin aminci za ka fāɗi.


Amma ni, ina yin abin da yake daidai, Ka yi mini jinƙai ka fanshe ni!


Na yage mulki daga gidan Dawuda na ba ka, duk da haka ba ka zama kamar bawana Dawuda ba, wanda ya kiyaye umarnaina, ya bi ni da zuciya ɗaya, yana yin abin da yake daidai a gare ni.


Idan za ka kasa kunne ga duk abin da na umarce ka, ka bi tafarkuna, ka aikata abin da yake daidai a gare ni, ka kiyaye dokokina da umarnaina kamar yadda bawana Dawuda ya yi, zan kasance tare da kai, zan sa gidanka ya kahu kamar yadda na sa gidan Dawuda ya kahu, zan ba ka Isra'ila.


Ka hurta rashin laifina, ya Ubangiji, Gama na yi abin da suke daidai, Na dogara gare ka gaba ɗaya.


Sai dai mutumin da yake biyayya ga Allah da kowane abu, Yana kuwa aikata abin da yake daidai, Wanda yake faɗar gaskiya da zuciya ɗaya,


Yanzu fa, ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ka cika wa bawanka Dawuda, tsohona, sauran abin da ka alkawarta masa, da ka ce, ‘Ba za ka rasa mutum a gabana wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba, in dai zuriyarka sun mai da hankali, sun yi tafiya a gabana kamar yadda kai ka yi.’


“Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuna aikata dukan umarnansa waɗanda nake umartarku da su yau, to, Ubangiji Allahnku zai fifita ku fiye da dukan sauran al'umma.


'Ya'yan da mahaifinsu amintacce ne, wanda yake aikata abin da yake daidai, sun yi sa'a.


Amintaccen mutum zai zauna lafiya ba abin da zai same shi, amma marasa aminci za a kama su.


Ba shi ya faɗa mini, ‘Ita 'yar'uwata ce’ ba? Ba ita kanta kuma ta ce, ‘Shi ɗan'uwana ne’ ba? Cikin mutunci da kyakkyawan nufi na aikata wannan.”


Sulemanu ya ƙaunaci Ubangiji, ya yi tafiya bisa ga koyarwar tsohonsa, Dawuda, amma ya miƙa sadakoki da hadayu da yawa a al'amudai dabam dabam.


Sulemanu ya amsa ya ce, “Kai ne kake nuna ƙauna mai girma a koyaushe ga bawanka Dawuda, tsohona, domin ya yi tafiya a gabanka da aminci, da adalci, da tawali'u. Kai kuwa ka tabbatar masa da wannan ƙauna mai girma, ka kuma ba shi ɗa wanda zai hau gadon sarautarsa a wannan rana.


“Idan ka yi biyayya da dokokina da umarnaina, to, zan cika maka alkawarin da na yi wa tsohonka Dawuda.


“Ka tuna da ni yanzu, ya Ubangiji, ina roƙonka, da yadda na yi tafiya a gabanka da aminci, da zuciya ɗaya, na aikata abin da yake mai kyau a gabanka.” Sai ya yi ta rusa kuka.


Dawuda kuwa ya lura da su da zuciya ɗaya, Da gwaninta kuma ya bi da su.


Abin da nake yi ba zai zama laifi ba, Yaushe za ka zo wurina? Da zuciya mai tsabta zan zauna a gidana.


Mai farin ciki ne wanda yake tsoron Ubangiji, Wanda yake zamansa bisa ga umarnansa!


Gama na kiyaye dokar Ubangiji, Ban yi wa Allahna tayarwa ba.


Ya nemi Allah na ubansa, ya bi umarnansa. Bai bi halin Isra'ila ba.


wanda yake bin dokokina, yana kuma kiyaye ka'idodina da aminci, shi adali ne. Hakika zai rayu, ni Ubangiji na faɗa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ