Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 9:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ubangiji ya ce masa, “Na ji addu'arka da roƙe-rokenka da ka yi a gare ni, saboda haka na tsarkake Haikalin nan da ka gina, na kuma sa sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata kuma za su kasance a wurin kullum.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Ubangiji ya ce masa, “Na ji addu’arka da kuma roƙon da ka yi a gabana; na tsarkake wannan haikali wanda ka gina, ta wurinsa Sunana zai kasance a can har abada. Idanuna da zuciyata kullum za su kasance a can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 9:3
30 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wannan ita ce amincewarmu a gabansa, wato, in mun roƙi kome bisa ga nufinsa, sai ya saurare mu.


Za ka saurara ga addu'o'in masu kaɗaici, ya Ubangiji, Za ka ba su ƙarfin hali.


“Ka koma, ka faɗa wa Hezekiya sarkin jama'ata cewa, ‘Ni Ubangiji Allahn kakanka, Dawuda, na ji roƙonka, na kuma ga hawayenka, saboda haka zan warkar da kai, a rana ta uku kuwa za ka haura zuwa Haikalin Ubangiji.


Domin ka riƙa duban Haikalin nan dare da rana, wurin da ka ce sunanka zai kasance domin ka riƙa jin addu'ar da bawanka zai yi yana fuskantar wurin.


Ina ƙaunar Ubangiji, saboda yana jina, Yana kasa kunne ga addu'o'ina.


Ƙasa ce kuma wadda Ubangiji Allahnku yake lura da ita, Ubangiji Allahnku yana dubanta kullum, tun daga farkon shekara har zuwa ƙarshenta.


“Yanzu fa, ya Allahna, ina roƙonka, ka buɗe idanunka, ka kasa kunnuwanka, ka saurari addu'ar da ake yi a wannan wuri.


ya ce, ‘Ya Karniliyas, an amsa addu'arka sadakarka kuma ta zama abar tunawa ga Allah.


Saboda haka sai ku yi addu'a kamar haka, “ ‘Ya Ubanmu, wanda yake cikin Sama, A kiyaye sunanka da tsarki.


Gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama, da duniya, da teku, da dukan abin da yake cikinsu, amma a rana ta bakwai ya huta. Soboda haka Ubangiji ya keɓe ranar Asabar, ya tsarkake ta.


A lokacin da ka fara roƙe-roƙenka sai aka ba da umarni, na kuwa zo domin in faɗa maka, gama ana sonka ƙwarai. Sai ka fahimci maganar da wahayin.


Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da a ce Musa da Sama'ila za su tsaya a gabana, duk da haka zuciyata ba za ta komo wurin mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana su yi tafiyarsu!


Sai ku yi murna a gaban Ubangiji Allahnku a inda Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya tabbatar da sunansa, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Balawen da suke zaune a garinku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune tare da ku.


sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa ya sa sunansa.


Waɗannan farantan ƙona turaren sun zama tsarkakakku sa'ad da aka miƙa su a bagaden Ubangiji. Sai ka ɗauki farantan mutanen da suka yi zunubin da ya jawo, musu mutuwa, ka ƙera murfin bagade da su, gama an miƙa su a gaban Ubangiji, ta haka za su zama gargaɗi ga jama'ar Isra'ila.”


Ko dā ma na sani koyaushe kana saurarona, amma na faɗi haka ne saboda jama'ar da suke nan tsaitsaye, domin su gaskata kai ne ka aiko ni.”


Amma hakika Allah ya ji ni, Ya saurari addu'ata.


Idan wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya sa sunansa ya yi muku nisa ƙwarai, to, sai ku yanka daga cikin garken shanunku, ko daga tumaki da awaki, waɗanda Ubangiji ya ba ku, kamar yadda na umarce ku. Za ku iya ci yadda kuke bukata a garuruwanku.


Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin kabilanku duka, inda zai sa sunansa, ya mai da shi wurin zamansa.


Siffar gunkiyan nan Ashtoret wadda ya yi, ya kafa ta a Haikalin da Ubangiji ya ce wa Dawuda da ɗansa Sulemanu, “A cikin wannan Haikali a Urushalima wadda na zaɓa daga cikin dukan kabilan Isra'ila zan tabbatar da sunana har abada.


Sai ya kafa gunkin da ya yi a cikin Haikalin Allah, wanda Allah ya faɗa wa Dawuda da ɗansa Sulemanu ya ce, “A cikin wannan Haikali da a Urushalima, inda na zaɓa daga cikin dukan kabilan Isra'ila, zan sa sunana har abada.


Allah wanda ya sa sunansa ya kasance a Urushalima, ya hamɓarar da kowane sarki, ko al'umma waɗanda za su sāke wannan doka don su lalatar da Haikalin Allah da yake a Urushalima. Ni Dariyus na kafa wannan doka. Lalle ne a kiyaye dokata sarai.”


Adalai sukan yi kira ga Ubangiji, yakan kuwa kasa kunne, Yakan cece su daga dukan wahalarsu.


Zan tsarkake alfarwa ta sujada da bagaden, zan kuma tsarkake Haruna da 'ya'yansa maza don su zama firistoci masu yi mini aiki.


Zunubanmu sun kāshe mu, Amma za ka gafarta zunubanmu.


Sa'an nan za ku zo ku tsaya a gabana a wannan Haikali, wanda ake kira da sunana, ku ce, “An cece mu,” don kawai ku ci gaba da yin dukan waɗannan abubuwan banƙyama?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ