Hiram, Sarkin Taya, kuwa ya ba Sulemanu katakan itacen al'ul da na fir da zinariya, iyakar yadda yake bukata. Sarki Sulemanu kuwa ya ba Hiram garuruwa ashirin a jihar Galili.
Dukan finjalai na sarki Sulemanu, da zinariya aka yi su, haka kuma finjalan da suke cikin ɗakin da aka gina da katakai daga Lebanon, ba a yi wani finjali da azurfa ba, domin ba a mai da azurfa kome ba a kwanakin Sulemanu.
Sa'an nan Sarauniyar Sheba ta ba sarki talanti ɗari da ashirin na zinariya, da kayan yaji mai yawan gaske, da duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kawo kayan yaji da yawa kamar yadda Sarauniyar Sheba ta kawo wa sarki Sulemanu ba.