1 Sarakuna 8:66 - Littafi Mai Tsarki66 A rana ta takwas ya sallami jama'ar, su kuwa suka yabi sarki. Sa'an nan suka kama hanyar gidajensu suna murna, suna farin ciki saboda dukan alherin da Ubangiji ya yi wa bawansa, Dawuda, da jama'arsa, Isra'ilawa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202066 A rana ta biye sai ya sallame mutane. Suka sa wa sarki albarka, sa’an nan suka watse zuwa gida, da farin ciki, da murna a zukatansu saboda kyawawan abubuwan da Ubangiji ya yi domin bawansa Dawuda, da kuma mutanensa Isra’ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |