1 Sarakuna 8:63 - Littafi Mai Tsarki63 Sulemanu kuwa ya miƙa wa Ubangiji hadaya ta salama da bijimai dubu ashirin da dubu biyu (22,000) da tumaki dubu ɗari da dubu ashirin (120,000). Ta haka sarki da dukan mutanen Isra'ila suka keɓe Haikalin Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202063 Solomon ya miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, shanu dubu ashirin da biyu, tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan Isra’ilawa suka keɓe haikalin Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga shi dai, na yi niyyar gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe masa shi, domin a riƙa ƙona masa turare mai daɗin ƙanshi, inda kuma za a riƙa ajiye gurasar ajiyewa dukan lokaci, don kuma a riƙa miƙa hadayun ƙonawa safe da yamma, da ranakun Asabar, da na amarya wata, da kuma a lokatan ƙayyadaddun idodin Ubangiji Allahnmu, yadda dai aka faralta a riƙa yi a cikin Isra'ila.