Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 8:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Sarki Sulemanu kuwa tare da dukan taron jama'ar Isra'ila, waɗanda suka taru a gabansa, suna tare a gaban akwatin alkawari, suna ta miƙa sadakoki, da tumaki, da bijimai masu yawa, har ba su ƙidayuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 sai Sarki Solomon da dukan taron Isra’ila da suka tattaru kewaye da shi a gaban akwatin alkawari, suka yi ta miƙa hadayar tumaki da bijimai masu yawa da ba a iya lissaftawa, ko ƙirgawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 8:5
6 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da masu ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji suka yi tafiya taki shida, sai Dawuda ya yi hadaya da sa, da keɓaɓɓiyar tunkiya.


Suka fa shigo da akwatin alkawarin Allah, suka ajiye shi a cikin alfarwar da Dawuda ya kafa masa, suka miƙa hadayu na ƙonawa da na salama a gaban Allah.


Yerobowam kuma ya sa a yi idi ran goma sha biyar ga wata na takwas kamar yadda ake yi a Yahuza. Ya miƙa hadayu bisa bagade, haka ya yi a Betel. Ya yi ta miƙa hadayu ga siffofin maruƙan da ya yi. Ya kuma sa firistoci a masujadan da ya gina a Betel.


Sulemanu kuwa ya haura, ya tafi wurin da bagaden tagulla yake a gaban Ubangiji, a cikin alfarwa ta sujada, ya miƙa hadayun ƙonawa dubu a kansa.


Dabbobi suna nishi! Garkunan shanu sun ruɗe Domin ba su da makiyaya. Garkunan tumaki da awaki kuma suna shan azaba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ