Wannan ya yi nesa da kai, da ka aikata irin haka, wato da za ka aza mai adalci daidai yake da mugu! Wannan ya yi nesa da kai! Mahukuncin dukan duniya ba zai yi adalci ba?”
Sun yi ƙiba, sun yi bul-bul, Ba su da haram a kan aikata mugunta, Ba su yi wa marayu shari'ar adalci, don kada su taimake su. A wajen shari'a ba su bin hakkin matalauta.
“Idan jama'arka sun tafi su yi yaƙi da abokan gābansu, idan sun yi addu'a a gare ka, suna fuskantar birnin nan da ka zaɓa, da Haikalin nan wanda na gina saboda sunanka,
“Idan jama'arka sun yi maka zunubi, gama ba mutumin da ba ya yin zunubi, har ka yi fushi da su, ka kuwa bashe su a hannun abokan gāba, har suka kwashe su zuwa bauta a wata ƙasa mai nisa,