1 Sarakuna 8:29 - Littafi Mai Tsarki29 Domin ka riƙa duban Haikalin nan dare da rana, wurin da ka ce sunanka zai kasance domin ka riƙa jin addu'ar da bawanka zai yi yana fuskantar wurin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202029 Bari idanunka su buɗe, su fuskanci wannan haikali dare da rana, wannan wurin da ka ce, ‘Sunana zai kasance a can,’ saboda ka ji addu’ar bawanka in yana fuskantar wannan wuri. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Rehobowam ɗan Sulemanu ya yi mulki a Yahuza. Yana da shekara arba'in da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta. Ya kuwa yi shekara goma sha bakwai yana sarauta a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga cikin kabilan Isra'ila duka, domin ya sa sunansa ya kasance a wurin. Sunan tsohuwarsa Na'ama, ita kuwa Ba'ammoniya ce.