Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 8:28 - Littafi Mai Tsarki

28 Duk da haka, ya Ubangiji Allahna, ka ji addu'ata, ni bawanka, da roƙe-roƙena, ka ji kukana da addu'ata da nake yi a gabanka yau.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

28 Duk da haka ka ji addu’ar bawanka da kuma roƙonsa don jinƙai, ya Ubangiji Allahna. Ka ji kuka da addu’ar da bawanka yake yi a gabanka a wannan rana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 8:28
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne?


Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu'a, kada kuma su karai.


Ka karɓi addu'ata kamar turaren ƙonawa, Ka karɓi ɗaga hannuwa sama da na yi kamar hadayar maraice.


Kai ne Allahna, saboda haka ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, Ina yin addu'a a gare ka dukan yini.


Ka kasa kunne ga kalmomina, ya Ubangiji, Ka kuma ji ajiyar zuciyata.


Ka amsa mini sa'ad da na yi kira, Ya Allah, madogarata! Lokacin da nake shan wahala, ka zama mai taimakona. Ka yi mini alheri, ka kuma saurari addu'ata!


Duk da haka ka kula da addu'ar bawanka da roƙe-roƙensa. Ya Ubangiji Allahna, ka kasa kunne ga kuka da addu'ar da bawanka yake yi a gabanka.


Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu'a da roƙo, tare da gode wa Allah.


Amma Ubangiji ya nuna musu alheri, ya ji tausayinsu, bai ba su baya ba saboda alkawarinsa da Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Bai yarda ya hallaka su ba, bai kuma yi watsi da su ba har wa yau.


ina roƙonka ka kasa kunne, ka kuma buɗe idanunka, ka ji addu'ar bawanka, wadda nake yi a gabanka dare da rana saboda bayinka, mutanen Isra'ila. Ina hurta zunubanmu, mu mutanen Isra'ila, da muka yi maka. Ni da gidan ubana mun yi zunubi.


Ya Sarkina, Allahna, Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ