Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 8:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Yanzu fa, ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ka cika wa bawanka Dawuda, tsohona, sauran abin da ka alkawarta masa, da ka ce, ‘Ba za ka rasa mutum a gabana wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba, in dai zuriyarka sun mai da hankali, sun yi tafiya a gabana kamar yadda kai ka yi.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 “Yanzu, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bari ka cika wa bawanka Dawuda mahaifina alkawaran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza sun yi hankali cikin dukan abubuwan da suke yi, don su yi tafiya a gabana kamar yadda ka yi.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 8:25
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

domin Ubangiji ya cika maganar da ya faɗa mini cewa, ‘Idan 'ya'yanka suna lura da hanyarsu, sun yi tafiya a gabana da gaskiya da zuciya ɗaya, da dukan ransu, ba za ka rasa mutum wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba.’


“Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.


Kai wanda ka cika abin da ka faɗa wa bawanka, Dawuda, tsohona, i, abin da ka faɗa da bakinka ka cika shi yau.


Ƙaƙa saurayi zai kiyaye ransa da tsarki? Sai ta wurin biyayya da umarnanka.


Sulemanu ya ƙaunaci Ubangiji, ya yi tafiya bisa ga koyarwar tsohonsa, Dawuda, amma ya miƙa sadakoki da hadayu da yawa a al'amudai dabam dabam.


Idan 'ya'yanka maza za su amince da alkawarina, Da umarnan da na yi musu, 'Ya'yansu maza kuma za su bi bayanka su zama sarakuna, A dukan lokaci.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ