1 Sarakuna 8:23 - Littafi Mai Tsarki23 ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ba wani Allah kamarka cikin Sama a bisa, da cikin duniya a ƙasa, wanda yake cika alkawari, ya nuna ƙauna ga bayinsa, waɗanda suke tafiya a gabansa da zuciya ɗaya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202023 ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama can bisa, ko a ƙasa can ƙarƙashi, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna ga bayinka waɗanda suke cin gaba a hanyarka da dukan zuciyarsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ya Allah, Allahnmu, da girma kake! Kai mai banrazana ne, cike da iko! Da aminci ka cika alkawaranka da ka alkawarta. Daga lokacin da Sarkin Assuriya ya danne mu, Har yanzu ma, wace wahala ce ba mu sha ba! Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu, Da annabawanmu, da kakanninmu, Da dukan sauran jama'arka sun sha wahala. Ka san irin wahalar da muka sha.