1 Sarakuna 7:40 - Littafi Mai Tsarki40-45 Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe da manyan cokula, da daruna. Haka Huram ya gama dukan aikin da ya yi wa Sulemanu a cikin Haikalin Ubangiji. Ga abin da ya yi. ginshiƙai biyu dajiya da take a kawunan ginshiƙan raga biyu don rufe dajiyar da take a kawunan ginshiƙai siffofin rumman ɗari huɗu domin raga biyu ɗin, da jeri biyu na siffofin rumman domin kowace raga don a rufe dajiyar da take a kawunan ginshiƙan dakalai goma daruna goma a kan dakalan kwatarniya ɗaya siffofin bijimai guda goma sha biyu da kwatarniya take zaune a kai, tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da kwanoni. Dukan kayayyakin aiki a cikin Haikalin Ubangiji waɗanda Huram ya yi wa sarki Sulemanu, an yi su ne da gogaggiyar tagulla. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202040 Ya kuma yi kwanoni da manyan cokula da kuma kwanonin yayyafawa. Ta haka Huram ya gama dukan aikin da ya yi wa Sarki Solomon a haikalin Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |