Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 7:39 - Littafi Mai Tsarki

39 Ya kafa dakali biyar a gefen dama na Haikalin, ya kuma kafa biyar a gefen hagu na Haikalin. Ya kuma sa kwatarniya na zubi a gefen dama na Haikalin, wajen kusurwar gabas maso kudu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

39 Ya sa dakalai biyar a gefen kudu na haikali, biyar kuma a arewa. Ya sa kwanon a gefen kudu, a gefen kudu maso gabas na haikalin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 7:39
6 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya girka kwatarniya a kusurwar kudu maso gabas daura da Haikalin.


Ya kuma yi daro goma na wanki, ya ajiye biyar a wajen kudu, biyar kuma a wajen arewa, don a riƙa ɗauraye abubuwan da ake hadayar ƙonawa da su. Amma kwatarniya don firistoci su riƙa wanka a ciki ne.


Ya kuma yi daruna na tagulla guda goma. Kowane daro yana cin misalin garwa tamanin. Kowane daro kamu huɗu ne. Kowane dakali yana da daro ɗaya.


Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe da manyan cokula, da daruna. Haka Huram ya gama dukan aikin da ya yi wa Sulemanu a cikin Haikalin Ubangiji. Ga abin da ya yi. ginshiƙai biyu dajiya da take a kawunan ginshiƙan raga biyu don rufe dajiyar da take a kawunan ginshiƙai siffofin rumman ɗari huɗu domin raga biyu ɗin, da jeri biyu na siffofin rumman domin kowace raga don a rufe dajiyar da take a kawunan ginshiƙan dakalai goma daruna goma a kan dakalan kwatarniya ɗaya siffofin bijimai guda goma sha biyu da kwatarniya take zaune a kai, tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da kwanoni. Dukan kayayyakin aiki a cikin Haikalin Ubangiji waɗanda Huram ya yi wa sarki Sulemanu, an yi su ne da gogaggiyar tagulla.


Sa'an nan ya yi alkuki goma na zinariya kamar yadda aka tsara. Ya sa su cikin Haikali, biyar a sashen dama, biyar kuma a hagu.


Sulemanu ya kammala dukan aikin Haikalin Ubangiji. Sa'an nan ya kawo kayayyakin da tsohonsa Dawuda ya riga ya keɓe, wato azurfa da zinariya, da dukan kayan girke-girke, da tasoshi, ya ajiye su a taskokin Haikalin Allah.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ